Isa ga babban shafi
Amurka

Biden ya ba da umarnin sakin bayanan sirri kan harin 9/11

Shugaban Amurka Joe Biden ya ba da umarnin sakin wasu bayanan sirri dangane da binciken gwamnati kan harin ta'addancin ranar 11 ga watan satumban da aka kaiwa kasar a shekarar 2001.

Hayaki yana fitowa bayan kone tagwayen hasumiyar Cibiyar Ciniki ta Duniya da jiragen da aka yi garkuwa da su, wadanda aka yi amfani da su wajen kai har ikan gine-ginen a birnin New York. Satumba 11, 2001.
Hayaki yana fitowa bayan kone tagwayen hasumiyar Cibiyar Ciniki ta Duniya da jiragen da aka yi garkuwa da su, wadanda aka yi amfani da su wajen kai har ikan gine-ginen a birnin New York. Satumba 11, 2001. AP - Richard Drew
Talla

Yayin sanar da umarnin, shugaban Amurkan ya ce za a fitar da bayanan cikin watanni shida masu zuwa.

Dangin wasu daga cikin kusan mutane dubu 3,000 da suka mutu a harin na Al-Qaeda sun dade suna neman bayyana wasu sirrikan binciken da aka gudanar, bisa hujjar cewa takardun bayanan ka iya kunsar shaidar cewa gwamnatin Saudiya, na da alaka da maharan da suka rusa Cibiyar Ciniki ta Duniya da kuma ma’aikatar tsaro ta Pentagon.

Matakin na zuwa ne gabannin cika shekaru 20 da kai harin na ranar 11 ga watan Satumba a 2001, wanda ya tunzura shugaban Amurka na waccan lokaci George W. Bush wajen bada umurnin mamaye Afghanistan, inda Taliban ta baiwa shugaban Al-Qaeda Osama Bin Laden mafaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.