Ambaliyar ruwa ta halaka mutane 44 a Amurka
Ambaliyar ruwan da guguwar Ida ta haddasa ta kashe akalla mutane 44 a jihohi hudu na arewa maso gabashin Amurka a tsakanin ranakun Laraba zuwa Alhamis, iftila’in da kwararru suka danganta da sauyin yanayi.
Wallafawa ranar:
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da guguwar ta Ida ta dauko, ya haifar da gargadin gaggawa na ambaliyar ruwan da ba a taba gani ba a Birnin New York, wadda ta mayar da tituna tamkar koguna, zalika ambaliyar ta rufe tashohi da titunan jiragen kasa na karkashin kasa.
Tuni dai shugaban Amurka Joe Biden ya ayyana dokar ta baci tare da bada umarnin fara ayyukan agaji na gaggawa a jihohin New York da New Jersey a ranar Alhamis.
Ambaliyar ruwa ta mamaye manyan hanyoyi a fadin gundumomin New Jersey da New York da suka hada da Manhattan, The Bronx da Queens, inda motoci da dama suka nutse.
Gwamnan New Jersey Phil Murphy ya shaidawa manema labarai cewa akalla mutane 23 suka mutu sakamakon ambaliyar da ta biyo bayan guguwar Ida.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu