Isa ga babban shafi
Amurka - Ambaliya

Guguwar Ida gami da ambaliyar ruwa sun ratsa wasu jihohin Amurka

Shekaru 16 bayan faruwar guguwar Katrina wadda ta haddasa mummunar barna a yankin Lousiana dake Kudancin Amurka a ranar Lahadi wata sabuwar guguwar da aka yiwa suna Ida da masana suka kira mai gudun kilomita 240 a sa’a daya, ta isa yankin.

Guguwar Ida ta tafka barna a wasu jihohin Amurka 29/08/21.
Guguwar Ida ta tafka barna a wasu jihohin Amurka 29/08/21. VIA REUTERS - MICHAEL DEMOCKER
Talla

Sama da mutane dubu 400 ne suka rasa wutar lantarki a New Orleans bayan isar guguwar wadda ke dauke da ruwan sama wanda ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutum daya, ko da yake gudunta ya ragu a wannan Litinin zuwa mataki na 1 daga na 4 da akayi hasasge da farko.

Hukumar Kula da Yanayi ta Kasar Amurka ta ba da gargadi cewar guguwar dake dauke da ambaliyar ruwa zata shafi yankuna da dama, ciki har da garin Jean Lafitte, da ke kudu da New Orleans.

Shugaba Joe Biden, wanda ya bayyana Ida a matsayin "guguwa mai barazana ga rayuwa'', ya ayyanata a matsayin babban bala'i ga Louisiana, wadda ke ba ta damar samun tallafin gwamnatin tarayya.

Mutum daya ya mutu sakamakon faduwar bishiyar a Prairieville, mai nisan mil 60 arewa maso yammacin New Orleans, in ji ofishin Sheriff na Ascension Parish.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.