Isa ga babban shafi
Faransa - Ta'addanci

An gurfanar da Faransawa 7 da ake zargi da ta'addanci a shekarar 2016

Yau ake gurfanar da wasu Faransawa bakwai da aka tsare bisa da su bisa zargin zama ‘yan kungiyar ta’addanci, bayan da aka kwato manyan makamai a jajibirin gasar kwallon kafa ta Euro 2016 a birnin Paris na Faransa.

Jami'an tsaro a Faransa bayan harin ta'addanci a Nice ranar 29 ga watan Oktoban 2020.
Jami'an tsaro a Faransa bayan harin ta'addanci a Nice ranar 29 ga watan Oktoban 2020. REUTERS/Eric Gaillard/Pool
Talla

A watan Maris din shekarar 2016, 'Yan sanda suka gano bindigogi kirar AK-47 da kuma kananu a wani gida dake unguwar birnin Paris, wacce daya daga cikin matasan bakwai, Reda Kriket, mai shekara 39 ya karbi hayarta, da kuma wasu abubuwa masu fashewa da aka taba amfani da su yayin munanan hare-haren da aka kai Paris a watan Nuwamban shekarar 2015.

Tun a wancan lokacin aka kame Kriket, wanda aka danganta shi da mutumin da ake zargi da jagorantar hare-haren na Paris, bayan da hukumomi suka  kwashe makonni suna sanya ido a kansa, kuma aka tuhume shi da ayyukan ta’addanci.

Masu gabatar da kara dai sunyi amannar cewa yana shirin kisa hari ne kan filin wasa na gasar Euro 2016, wacce ta gudana a Faransa.

Shirin kafa kungiyar ta'addanci a Faransa

Bayan wasu ‘yan kwanaki,‘ ne kuma ‘yan sandan Holland suka cafke Bahri Anis mai shekaru 37 dan kasar Faransa da shima ake zargi cikin lamarin.

Masu binciken sun ce girman makaman da aka kama a yankin Argenteuil da ke kusa da Paris da kuma lokacin - kwanaki bayan harin da aka kai a filin jirgin saman Brussels da tashar jirgin kasa - ya nuna wani harin na “gabatowa”, amma ba su da masaniya kan inda ake Shirin kai harin.

Kriket da Bahri an yi imanin cewa sun taba zuwa Siriya a ƙarshen shekarar 2014 ko farkon 2015.

Bayaga Artil da Bahri akwai kuma karin wasu da ake zargi

Ana zargin mutanen biyu da dan kasar Algeria mai shekaru 43 da haihuwa, Abderrahmane Ameuroud, wanda aka gano kwayoyin halittar sa DNA a gidan dake Argenteuil, da laifin kafa kungiyar ta'addanci a madadin kungiyar IS.

Ana kuma zargin wasu mutane  hudu  masu shekaru tsakanin 38 zuwa 44 da taka rawa a shrin na ta’addanci.

To sai dai Kriket ya musanta zargin shirya kai hari, yana shaidawa masu binciken cewa ya yi niyyar sayar da makaman ne domin samun kudi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.