Isa ga babban shafi
Faransa

Shekara guda da kazamin harin ta’addanci a Paris

Yau ake cika shekara guda da kazamin harin ta’addancin da aka kai birnin Paris wanda ya hallaka mutane 130 ya kuma girgiza kasar Faransa baki daya.An dai kama mutane 8 da ake zargi da hannu wajen kitsa harin.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande REUTERS/Charles Platiau
Talla

Ranar 11 ga watan Nuwamba na shekarar da ta gabata ne wasu yan ta’adda suka kaddamar da munanan hare haren da suka hallaka mutane 130 a birnin Paris.

Cikin wuraren da aka kai harin, harda filin wasan Stade de France, da kuma wani shagon abinci da giya da maharan suka bude wuta suka kuma kashe mutane 39, kafin harin Bataclan wanda ya hallaka mutane 90 da suka je gidan rawa.

Jami’an tsaro sun dai kashe tara daga cikin maharan da kuma masu taimaka musu, yayin da aka kama wasu 8 inda ake tsare da su a Faransa da Belguim saboda rawar da suka taka a kai hare haren.

Salah Abdesalam, daya daga cikin wadanda ake tuhuma da kaddamar da harin, na hannun jami’an tsaro, sai dai rahotanni sun ce yaki bai wa masu bincike hadin kan da ya da ce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.