Isa ga babban shafi

An gano gungun da ke taima wa 'yan ta'addan Syria a Faransa

‘Yan sandan Faransa sun kame mutane 29 a wani samame da suka kai kan wata kungiya da ke samar da kudade ga ‘yan ta’adda a Syria.

Sullan kudin sadarwar Bitcoin ta intanet
Sullan kudin sadarwar Bitcoin ta intanet JACK GUEZ / AFP
Talla

Ofishin mai gabatar da kara na yaki da ta’addanci a Farasa ne ya bankado wata babbar hanya da ake hada-hadar kudade tsakanin Faransawa da ‘yan awa da dangi da ake zargi da ayyukan ta’addanci a kasar Syria.

Wannan lamari ya kai ga tuhumar mutane 55 a kananan hukumomin Faransa 26 tare da tsare mutane 26 daga cikinsu.

Shekara daya kenan da samar da wannnan hanyar acewar masu gabatar da kara, wadanda suka daura alhakin kafata kan wasu matasan Faranawa biyu masu kimanin shekaru 25, da suka je Syria a shekarar 2013, don marawa kungiyar al-Qaeda baya.

Binciken ya gano cewa, mutanen kan je shagunan saida taba ne, dake da alhakin sayar da jaridu da layukan sadarwa domin sayan sullan kudaden sadarwa na Bitcoin na tsakanin euro 10 zuwa 150, kafin a sauya zuwa farin kudi kuma kai tsaye ke shiga asusun ajiyar mahara masu ikirarin jihadin a Syria don kaucewa wa sa’idon bankuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.