Isa ga babban shafi
Lebanon-Faransa

Amnesty ta bukaci Faransa ta daina sayarwa Lebanon makamai

Kungiyar Amnesty International ta bukaci Faransa ta dakatar da sayarwa Lebanon makamai bisa kafa hujja da yadda aka yi amfani da nau’ikan makaman ciki har da harsasan roba da hayaki mai sanya hawaye kan dandazon ‘yan kasar da ke tsaka da zanga-zangar lumana a 2019.

Wasu masu zanga-zangar kalubalantar gwamnati a Lebanon.
Wasu masu zanga-zangar kalubalantar gwamnati a Lebanon. ANWAR AMRO / AFP
Talla

Amnesty cikin sanarwar da ta fitar ta ce makaman da Faransar ke sayarwa Lebanon na taimakawa wajen take hakkin bil’adama ta mabanbantan fuskoki.

Cikin sanarwar shugaban sashen da ke kula da hada-hadar makamai na Amnesty Aymeric Elluin ba wannan ne karon farko da Lebanon ke amfani da samfurin makaman na Faransa kan fararen hula ba, domin ko a zanga-zangar 2015 sai da jami’an tsaronta suka yi amfani da nau’in makaman wajen take hakkin bil’adama.

Tsawon shekaru Faransa ke matsayin babbar mai sayar da makamaki ga Lebanon wanda kasar kan yi amfani da su wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya, sai dai aka yi amfani da makaman yayin zanga-zangar watan Oktoban 2019 a cewa kungiyar bai kamata Faransar ta sake sayar da makami ga kasar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.