Isa ga babban shafi
Coronavirus

A shirye muke mu karbi alluran rigakafin Coronavirus a bainar jama'a - Obama

Tsaffin shugabannin Amurka da suka hada da Barack Obama da George W. Bush da Bill Clinton sun ce a shirye suke su karbi rigakafin cutar Coronavirus a bainar jama’a domin basu karfin gwuiwar karbar cutar.

Tsaffin shugabannin Amurka Barack Obama da George W. Bush
Tsaffin shugabannin Amurka Barack Obama da George W. Bush REUTERS/Kevin Lamarque/Files
Talla

A hirar da yayi da manaema labarai Obama ya ce muddin hukumar yaki da cututtuka ta bada umurnin amfani da maganin rigakafin, zai gabatar da kan sa domin karbar maganin.

Babban hafsan tsohon shugaba Bush yace shima a shirye yake ya karbi rigakafin, kamar yadda Bill Clinton shima ya sanar.

Tuni dai Birtaniya ta za ma kasar Turai ta farko da ta amince da alluran rigakafin cutar coronavirus da hadin gwiwar kamfanonin Pfizer da BioNTech suka samar, inda gwamnatin kasar ta bada damar soma amfani da maganin a makon gobe.

Gwajin karshe da aka yi kan maganin rigakafin da hadin gwiwar Pfizerda BioNTech ya samar a watan Nuwamban da ya kare, ya nuna cewar ingancin allurar ya kai kasha 95 cikin 100 wajen hana kamuwa da cutar coronavirus tsakanin mutane masu yawan shekaru da matasa ba kuma tare da fuskantar wata matsala ba.

Yanzu haka dai gwamnatin Birtaniyar ta yi odar alluran rigakafin annobar ta coronavirus miliyan 40, wadanda za su isa a baiwa akalla mutane miliyan 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.