Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya kawo karshen cece-kuce kan lafiyarsa

A karon farko shugaban Amurka Donald Trump ya fita bainar jama’a tun bayan da ya koma fadar White House a Litinin da ta gabata, bayan shafe kwanaki uku a asibiti dalilin kamuwa da cutar coronavirus.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump Tom Brenner/Reuters
Talla

Yayin ganawa da mutane daga saman wata farfajiya a fadar White House, Trump wanda baya sanye da takunkumin rufe baki da hanci, ya shaidawa jama’a cewar garau yake jin jikinsa a yanzu, inda ya sha alwashin ganin bayan annobar coronavirus da ya bayyana da kwayar cutar China.

Ranar Litinin 12 ga watan Oktoba ake sa ran shugaba Trump ya yi tattaki zuwa jihar Florida domin cigaba da yakin neman wa’adi na 2, a zaben shugabancin Amurka da ke tafe ranar 3 ga watan Nuwamba, inda zai fafata da tsohon mataimakin shugaban kasar Joe Biden.

A ranar 2 ga watan Oktoba gwaji ya tabbatar Trump ya kamu da coronavirus dalilin da ya sanya shi kwanciya a asibiti tsawon kwanaki 3 gabanin ya sallami kansa daga asibitin ba tare da sahalewar likitoci ba, batun da ya haddasa cece-kuce.

A yanzu kuma gwajin bai tabbatar da Donald Trump ya rabu da cutar ba, sai dai bayanai sun ce ya daina nuna alamominta daidai lokacin da cutar ta halaka Amurkawa fiye da dubu 210.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.