Isa ga babban shafi

China ta aike wa Biden sakon taya murna

China ta aike da sakon taaya murna ga zababben shugaban Amurka Joe Biden, mako guda bayan an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar, tana mai cewa, ta girmama zabin Amurkawa.

Shugaban China, Xi Jiping da Joe Biden a  shekarar 2015 a birnin Washington.
Shugaban China, Xi Jiping da Joe Biden a shekarar 2015 a birnin Washington. PAUL J. RICHARDS / AFP
Talla

Dangantaka tsakanin Amurka da China ta yi tsami a ‘yan shekarun baya bayan nan a karkashin mulkin shugaba mai barin gado Donald Trump, kuma ba a taba samun haka ba tun da kassashen biyu suka fara hulda a hukumance, shekaru 40 da suka wuce.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, Wang Wenbin ya fada a wani taron manema labarai cewa lallai kasar na taya Joe Biden da Kamala Harris murnar lashe wannan zabe.

Kafin yanzu, China na cikin wasu manyan kasashen da ba su taya zababben shugaban Amurka murna ba kamar su Rasha da Mexico.

Tun da kafafen yada labran Amurka suka sanar da wanda ya samu kuri’u mafi yawa a zaben shugaban Amurka, shugaba mai barin gado Donald Trump bai amince da shan kaye ba akasin yadda aka saba yi a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.