Donald Trump ya cacaki China a taron MDD
Shugaban Amurka Donald Trump ya cacaki China a taron Majalisar Dinkin Duniya inda ya zarge ta da yadawa duniya annobar korona wadda yanzu haka ta lakume rayukan mutane kusan miliyan guda.
Wallafawa ranar:
Shugaba Donald Trump yace ya zama dole China ta dauki alhakin yada cutar korona a duniya.
Tuni kasar China ta maida martani wajen zargi shugaba Donald Trump da yada annobar siyasa a taron Majalisar Dinkin Duniya, jim kadan bayan ya cacaki kasar a jawabin da ya gabatar.
Jakadan China a Majalisar, Zhang Jun, yace a daidai lokacin da kasashen duniya suka mayar da hankali wajen yaki da annobar COVID-19, kasar Amurka ta mayar da hankali ne wajen yada cutar siyasa.
Jakadan yace ya zama dole ya jaddada cewar, surutun da Amurka keyi a Majalisar bashi da tasiri dangane da taron dake gudana yanzu haka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu