Isa ga babban shafi
Peru-Coronavirus

Magajin gari yayi mutuwar karya don gujewa hukunci kan laifin karya dokar hana fita

Magajin garin Tantara dake kudancin kasar Peru, Jamie Torres, yayi mutuwar karya domin gujewa kamun jami’an tsaro bayan samunsa da laifin karya dokar hana fitar dake aiki a kasar don dakile yaduwar annobar coronavirus.

Jaime Rolando Urbina Torres Magajin garin Tantara, bayan yin mutuwar karya don kamen jami'an tsaro.
Jaime Rolando Urbina Torres Magajin garin Tantara, bayan yin mutuwar karya don kamen jami'an tsaro. Policía Nacional del Perú
Talla

Torres ya yanke shawarar fadawa cikin wani akwatin gawa ne yayinda yayi mankas da barasa, sanye da takunkumin rufe baki da hanci ya kuma dauke numfashi tamkar matacce a lokacin da jami’an ‘yan sanda suka shiga gidansa da nufin kama shi.

Jaridar Dailymail dake Birtaniya ta ruwaito cewar tun a makwannin da suka gabata, al’ummar garin na Tantara ke korafi kan cewar shugaban nasu bai dauki annobar coronavirus da muhimmanci ba, zalika bai damu da tabbatar da cewa an dauki matakan kare rayukan jama’a a garin ba, hakan ne kuma yasa shi fita da abokanansa zuwa wani gidan shan barasa, inda a nan ne jami’an tsaro suka gano shi.

Jami’an ‘yan sanda a yanzu haka na tuhumar magajin gari Jamie Torres da laifukan, karya dokar hana fita, karya sharadin tsarin bada tazara tsakanin mutane, da kuma rashin daukar matakin killace garin Tantara da yake shugabanta daga zirga-zirgar shige da fice.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.