Isa ga babban shafi
Peru

Kuczynski ya soma aiki a Peru

Sabon shugaban kasar Peru Pedro Pablo Kuczynski ya soma aiki a yau Alhamis, sai dai akwai kalubale da dama da ke gaban sabon shugaban wanda tsohon ma’aikacin Banki ne a Wall Street na Amurka.

Sabon Shugaban Peru Pedro Pablo Kuczynski
Sabon Shugaban Peru Pedro Pablo Kuczynski Reuters
Talla

Babban kalubalen da ke gaban sabon shugaban na Peru shi ne kokarin farfado tattalin arzikin kasar tare da hada kan al’ummar kasa musamman rabuwar kai da aka samu bayan kammala zaben shugaban kasa mai cike da kalubale.

A yakin neman zaben shi sabon shugaban ya ce zai kashe kudade da inganta saka jari tare da rage haraji, sannan ya yi alkawalin samar da ayyukan yi sama da miliyan guda

Amma Bankin Duniya ya yi kiyasin cewa kusan rabin mutanen Peru na rayuwa ne cikin talauci.

Ana ganin shugaban dole sai ya yi aiki tare da bangaren jam’iyyar adawa ta Kaiko Fujimori wanda ya doke a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan jiya.

Tuni dai shugaba Kuczynski ya kafa gwamnati da ta kunshi ‘yan boko zalla, amma sauran manyan kalubalen da ke gaban shi sun hada da kawo karshe kashe-kashe da fashi da makami.

Sannan da yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi inda Peru na cikin manyan kasashen da ake samar da hodar ibilis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.