Isa ga babban shafi

Coronavirus na haifar da cikas ga wasannin Italiya

Mai yiwuwa kungiyar Inter Milan ta buga wasanta na gasar Europa da zata karbi bakwancin Ludogorets ya kasance ba tare da ‘yan kallo ba, saboda fargabar yaduwar cutar coronavirus.

Kungiyar Inter Milan na Italia yayin murnar nasara kan AC milan a San Siro
Kungiyar Inter Milan na Italia yayin murnar nasara kan AC milan a San Siro Reuters/Daniele Mascolo
Talla

Inter Milan dai na daya daga cikin kungiyoyi hudu na gasar Serie A na Italia da suka dage wasanninsu na karshen mako.

Yanzu haka ana ta tattaunawa tsakanin kulob din, da jami'an gwamnatin Italiya da hukumar Uefa ta Turai dangane da wasan na ranar Alhamis.

Duba da kasancewar kasar Italiya kasar ta annobar cutar coronavirus tafi kamari a Nahiyar Turai, inda ta halla mutane 6 cikin 219 dake dauke da cutar.

A yau Litin da dama daga makarantu da kwalejoji a birnin Milan sun kasance a rufe, kodayake tsarin sufurin cikin gida na aiki.

Fiye da magoya bayan Club din Ludogorets sama da 600 ne za su yi tattaki daga Bulgaria don halartan wasan na kungiyoyi 32 a gasar Europa ranar Alhamis a San Siro.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.