Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Real Madrid ta yi wasanni 20 ba a doke ta ba

Real Madrid ta buga wasa na 20 ba tare da rashin nasara ba a wannan kaka, bayan ta doke Real Zaragoza ta wajen zazzaga mata kwallaye hudu ba tare da ta farke ko daya ba a wasan Copa del Rey da suka gwabza ranar Laraba.

'Yan wasan  Real Madrid a 2017.
'Yan wasan Real Madrid a 2017. REUTERS/Sergio Perez
Talla

Raphael Varane, Lucas Vazquez, Vinicius Junior da Karim Benzema ne suka ci kwallo a wannan wasa da aka kara a filin wasa na La Romareda, inda har ila yau Madrid ta buga wasan ba tare da ‘yan wasanta, Gareth Bale da Eden Hazard, wadanda da ke jinya ba, yayin Benzema kansa ya shigo wasan ne bayan hutun rabin lokaci.

Kusan ana da tabbacin cewa Benzema zai fara murza tamola tun daga farkon wasa a karawarsu da abokan hamayya Atletico Madrid a ranar Asabar mai zuwa, inda Real din za ta yi fatan ci gaba da baiwa abokan hamayya na birnin Catalonia, Barcelona tazarar maki 3 a saman teburin La liga.

Akasin yadda al’amarin ya kasance wa Barcelona, wadanda suka fara kakar da tangal - tangal a karkashin sabon koci Quique Setien, da kuma Atletico wadanda kusan kamar dabara ta kare musu a karkashin mai horarwa Diego Simeone, Madrid ta kasance kan ganiyarta a ‘yan makonin da suka wuce.

Bayan nasara kan Real Valladolid a ranar Lahadi, kocin Madrid Zinedine Zidane ya ta’allaka sirrin nasarar tawagarsa da masu tsaron baya da ke da amince da sanin makamar aiki.

Zalika, rashin saka ko da kwallo daya a ragar Real Madrid a Zaragoza na nufin ya zuwa yanzu kwallaye uku ne kawai suka taba musu zare a wasanni 9 da suka buga.

Ana ganin wannan shu’umancin na Real Madrid na iya yi musu rana a haduwar da zasu yi a mataki na kungiyoyi 16 a gasar zakarun nahiyar Turai, inda zasu kara da tawagar Pep Guardiola wato, Manchester City a wata mai kamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.