Isa ga babban shafi
Faransa

Ni zan karbi ragamar shugabancin Faransa a 2022- Le Pen

Jagorar Jam’iyyar masu tsattsauran ra’ayi a Faransa Marine Le Pen ta sha alwashin iya nasara kan shugaban kasar mai ci Emmanuel Macron yayin zaben da ke tafe a shekarar 2022, kalaman da ke zuwa dai dai lokacin da Macron ke fuskantar boren al’umma kan gyare-gyaren da ya ke shirin samarwa a kasar.

'Yar takarar neman kujerar shugabancin kasar Faransa, Marine Le Pen ta Jam'iyyar masu tsattsauran ra'ayi.
'Yar takarar neman kujerar shugabancin kasar Faransa, Marine Le Pen ta Jam'iyyar masu tsattsauran ra'ayi. Fuente: AFP.
Talla

A wani sakon sabuwar shekara da Le Pen ke gabatarwa jiya Alhamis ta ce har yanzu ta na da kyakkyawan fata kan al’ummar faransa wadanda ta ce yanzu haka suna dandana kudarsu.

A cewar Le Pen tuni ta sake bayyana kudirinta na sake tsayawa takarar neman kujerar shugabancin kasar ta Faransa, kuma ta na da yakinin za ta yi nasara a wannan karon.

Tsohuwar ‘yar takarar shugabancin kasar ta Faransa, Marine Le Pen ta ce fatanta hadin kan al’ummar Faransa tare da ci gaban kasar.

Le Pen wadda ta yi nasarar tsayawa takara a shekarar 2017 amma kuma ta fuskanci gagarumin shan kaye a hannun Emmanuel Macron ta ce babu shakka tarihi ba zai maimaita kansa, don kuwa a wannan karon ta na da kwarin gwiwar iya lashe zabe.

A cewarta yayin babban taron Jam’iyyarta ne cikin shekarra 2021 za ta kaddamar da yakin neman zabenta bayan zaben wanda zai tsayawa jam’iyyar tsakaninta daJordan Bardella.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.