An gurfanar da Marine Le Pen a gaban kotu
Bangaren shari’a a Faransa ya shigar da karar shugabar Jamiyar National Front Marine Le Pen bisa zargin yada hotunan da ba su dace ba ta kafar sadarwan Tweeter.
Wallafawa ranar:
Matakin da masu shigar da kara a Nanterre, da ke wajen birnin Paris ya biyo bayan da Majalisar kasar ta Faransa ta dauka ne a watan Nuwambar da ya gabata inda ta cire rigar kariya na wakiliyar majalisar saboda baza hotunan 3 a shekara ta 2015 na ayyukan ‘yan taadda na IS
A zaben bara dai Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya doke Marine Le Pen, lokacin da ta kara da shi a zaben shugabancin kasar.
Ana zargin ta da laifin yada hotunan ta’addanci da na batsa da ake ganin suna da hatsari ga mutane kasar.
Laifufukan na iya kai ga dauri na tsawon shekaru 3 gidan yari da kuma biyan tara ta kudin Turai Euro dubu 75, kwatankwacin kudin Amurka Dala dubu 91.
Marine Le Pen ta ki amincewa da zargin, inda take cewa da ace wata kasa ce, da har lambar zinari za’a ba ta saboda ta yada hoton ne domin nuna bakin ciki da ayyukan ‘yan kungiyar IS.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu