Isa ga babban shafi

kamfanin Google zai biya Faransa tarrar euro miliyan 500

Katafaren kamfanin sadarwar kasar Amurka Google ya amince ya biya tarrar euro miliyan 500 domin sasanta zargin da ake masa na kaucewa biyan haraji a Faransa.

Katafaren kamfanin sadarwar kasar Amurka Google ya amince ya biya tarrar euro miliyan 500 domin sasanta zargin da ake masa na kaucewa biyan haraji a Faransa
Katafaren kamfanin sadarwar kasar Amurka Google ya amince ya biya tarrar euro miliyan 500 domin sasanta zargin da ake masa na kaucewa biyan haraji a Faransa ©REUTERS/Aly Song/File Photo
Talla

Matakin ya biyo bayan wata yarjejeniya da aka cimma tsakanin Kamfanin Google da ma’aikatar tattara harajin kasar Faransa.

Google ya sanar da cewa ya kawo karshen matsalar kaucewa biyan harajin a tattaunawar da suka yi, inda suka amince da biyan euro miliyan 500 da wasu Karin euro miliyan 465.

Wannan matakin dai zai kawo karshen duk wata tuhuma ko zargin kaucewa biyan haraji da akewa kamfanin tun daga shekarar 2015.

A karkashin dokokin shari’a, duk wani kamfani da aka zarga ka iya bin hanyar tattaunawa don biyan tar aba tare da gurfana gaban kuliya ba, ballema kai ga tambayar aikata laifi ko a’a.

Tuni Ministatan shari'ar Faransa Nicole Galoubet da takwaransa na Kasafin kudi Gerald Darmanin sukayi maraba da matakin cimma dai-daito da aka samu, inda suka kara da cewa, matakin ya biyo bayan aiki tukuru na tsawon shekaru biyu da gwamnatin kasar tayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.