Kamfanin Google ya kare kansa daga zargin kin biyan kudin haraji
Shugaban Kamfanin Google Eric Schmidt ya kare kamfanin Yanar Gizon na kasar Amurka kan zargin kin biyan Haraji ga kasar Birtaninya. Shugaban Kamfanin dai ya kare zargin da ake yiwa Kamfanin ne a wani Rubutun da yayi a wata Jarida da ake kira Observer, inda yake cewar a kowane lokaci Google nada anniyar yin abinda ya yi dai dai da doka ne, ba yi mata karan tsaye ba.
Wallafawa ranar:
Ya kara da cewar Kamfanin na Google, ya kuma biya wasu kayyadaddun Kudade ga gwamnatin kasar Birtaniya a cikin Gida.
Idan ana iya tunawa a Satin daya gabata ne Shugabar wani Kwamitin kula da al’amurran da suka shafi al’umma na Majalisar kasar Birtaniya Margret Hodge ta bayyana Kamfanin Google a matsayin “Takadari” da baya son biyan haraji, a lokacin da mataimakin shugaban Kwamitin ke karba tambayoyin kwamitin.
Ta ce Google na tara kudi da suka kai Biliyan 4.9 na kuding Ingila a kowace shekara, amma kuma ya biya milliyan shuda ne kurum a shekarar 2011.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu