Isa ga babban shafi

Majalisar Faransa ta amince da sake gina Majami'ar Notre-Dame

‘Yan majalisun Faransa sun amince da kudirin dokar sake gina majami’ar Notre Dame cikin shekaru 5 masu zuwa, bayan kudirin hakan da shugaban kasa Emmanuel Macron ya shiga gabansu.

Wani bangare na Majami'ar Notre-Dame da wuta ta kona
Wani bangare na Majami'ar Notre-Dame da wuta ta kona REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Matakin majalisar kan amincewar da kudirin zai taimakawa shugaba Macron wanda ya sha alwashin sake gina majami’ar mafi kayatarwa fiye da wadda wuta ta kona ranar 15 ga watan Aprilu.

Yayin zama kan kudirin a yammacin jiya Juma’a ‘Yan Majalisu 32 sun mara baya ga shirin sake gina majami’ar yayinda wasu 5 suka kalubalanci kudirin sai kuma wasu 10 da suka kauracewa zaman.

Bisa amincewa da matakin hakan na nufin Faransar za ta kammala sake ginin Majami’ar nan da shekarar 2024 dai dai da lokacin da za ta karbi bakoncin gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya wato Olympics.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.