Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta karrama jami'an da suka kashe gobarar Notre Dame

Kwanaki uku bayan da mummunar gobarar da ta lakume Mujami’ar Notre Dame mai dumbin tarihi a birnin Paris na Faransa, shugaban kasar Emmmanuel Macron ya karrama daukacin wadanda suka taimaka wajen ceto mujami’ar masamman jami’an kashe gobara.

Cikin wadanda aka karrama har da wanda ya ceto rawanin-kayar da aka sanya wa Yesu Al-Masihu a lokacin gicciye shi
Cikin wadanda aka karrama har da wanda ya ceto rawanin-kayar da aka sanya wa Yesu Al-Masihu a lokacin gicciye shi REUTERS/Philippe Wojazer/File Photo
Talla

A yayin wani kasaitaccen biki a fadar Elysee, shugaba Macron ya gana da jami’an kwana-kwana 270 cikin 400 da suka yi aikin kashe gobarar da wasu jami’an ‘yan sanda har ma da wasu mutane da suka taka rawa wajen ceto mujami’ar  mai dauke da kayan tarihi.

A yayin jawabin bangirma, shugaba Macron ya jinjina musu kan gwarzontaka da kuma kwarewa da suka nuna yayin aikin kashen gobarar da gidajen talabijin suka nuna kai tsaye, kuma duniya ta shaida hakan, in da ya lakaya wa daukacin jami’an kashe gobarar lambar yabo ta kasa.

Wasu da Macron din ya tarbe su, sun mika godiyarsu ga shugaban, in da suka ce, abin alfahari ne yi wa kasa hidima kuma a yabe ka.

Cikin jami’an kwana-kwanan da aka karrama har da Chaplain Jean-Marc Fournier, wanda ya ceto rawanin kaya da ake zaton an sanya wa Yesu Al-Masihu a yayin gicciye shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.