Isa ga babban shafi
Faransa

Attajirai sun bayar da Euro miliyan 600 na sake gina Cocin Faransa

Attajirai da gwamnatocin kananan hukumomi sun yi alkawarin bayar da tallafin Euro miliyan 600 domin sa ke gina Mujami’ar Notre Dame da gobara ta cinye a Faransa.

Majami'ar Notre Dame da ta kama da wuta a Faransa
Majami'ar Notre Dame da ta kama da wuta a Faransa ©REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Kamfanin Samar da kayyakin ado na Kering ne ya fara bude fage da agajin Euro miliyan 100, yayinda rukunin kamfanin LVMH da ke gogayya da Kering shi ma ya yi alkawarin Euro miliyan 200.

Kazalika shugaban Kamfanin Mai na Total ya bayar da tabbacin bayar da Euro miliyan 100 daga bangarensu.

Har wa yau akwai attajirin nan mai zuba hannayen jari, wato Marc Ladreit de Lacharrierre da ya yi alkawarin bayar da Euro miliyan 10 , yayinda kamfanin gine-gine na Martin and Oliver Bouygues shi ma ya bayar da Euro miliyan 10.

A bangare guda, an samu wasu daidaikun mutane da cibiyoyi har ma da kungiyoyi da suka boye sunayensu da suma suka bayar da gudunmawarsu ta jumullar Euro miliyan 1.6, yayinda magajiyar birnin Paris, Anne Hidalgo ta ce, za su bayar da Euro milyan 50.

Tuni shugabannin kasashen duniya da suka hada da Amurka da Rasha da China da Birtaniya da fadar Vatican har ma daga nahiyar Afrika suka jajanta kan aukuwar gobarar a ginin Mujami’ar mai shekaru kusan 900.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.