Isa ga babban shafi
Birtaniya-Turai

Zabin ficewa ba tare da yarjejeniya ba kadai ya ragewa Birtaniya - EU

Shugabannin kasashen Turai sun tsananta matsin lamba ga 'yan majalisar dokokin Birtaniya don ganin sun goyi bayan yarjejeniyar ficewar kasar daga EU da suka cimma da Firaminista Theresa May, inda suka gargadi Majalisar da cewa zabin da ya rage shi ne ficewa daga kungiyar ba tare da yarjejeniya ba.Kalaman na EU na zuwa ne bayan Theresa May ta mika bukatar jinkirta wa'adin ficewar kasar daga EU gaban shugabancin kungiyar da ke Brussels.

Yanzu haka Theresa May ta fara halartar taron na Brussels tare da sauran shugabannin kasashen kungiyar 27
Yanzu haka Theresa May ta fara halartar taron na Brussels tare da sauran shugabannin kasashen kungiyar 27 Olivier Hoslet/Pool via REUTERS/File Photo
Talla

Kwanaki Takwas cal gabanin kammala warwarewar alaka tsakanin Birtaniyar da EU ne, Theresa May ta bukaci kara wa'adin ficewar sabanin yadda aka tsara tun farko, wato ranar 29 ga watan Maris na shekarar nan.

Sauran kassahen kungiyar ta EU dai kawo yanzu na cike da fargabar yiwuwar samun nasarar Theresa May gaban Majalisa kan yarjejeniyar da ta kulla da EU, ciki har da shugaban Faransa Emmanuel Macron da ya sake jaddadawa Majalisar cewa wannan ce dama ta karshe ga Majalisar.

Tun a jiya Laraba ne, Theresa May ta aikewa shugaban hukumar Tarayyar Turai Donal Tusk bukatar a jinkirta mata wa'adin ficewar zuwa ranar 30 ga watan Yuni.

Tuni dai Donald Tusk ya tsegunta cewa mai yiwuwa sauran kasashen kungiyar 27 su amince da bukatar ta May don ba ta damar samun amincewar Majalisar Birtaniya.

Sai dai Donald Tusk ya ce ba shakka batun ya fara gundurar shugabannin Turai, kuma ya na fargabar fatarsa ta cewa za su daga kafa na iya zama almara.

Sau biyu kenan dai Majalisar dokokin Birtaniya na sa kafa ta na shure kunshin yarjejeniyar ta Theresa May da ta cimma da EU batun da ke sanya fargabar yiwuwar kammala ficewar kasar daga EU salin-alin.

A ranar Alhamis din nan, yayin wani taron mai sarkakiya na Majalisar Tarayyar Turai, Theresa May za ta samu damar gabatar da bukatunta, sai dai wakilan Turan sun jaddada cewa babu wata matsaya da za a cimma har sai mako mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.