Isa ga babban shafi
Birtaniya

Birtaniya na son a jinkirta mata ficewa daga Turai

Firaministar Birtaniya, Theresa May za ta bukaci jinkirta ficewar kasar daga gungun kasashen Turai a cikin wata wasika da za ta aika wa Kungiyar Tarayyar Turai a ranar Laraba.

Firaministar Birtaniya Theresa May
Firaministar Birtaniya Theresa May Reuters TV via REUTERS
Talla

Wannan jinkiri ya haifar da rashin tabbas game da ficewar Birtaniya cikin tsanaki, in da yanzu haka kasar ke da zabin ficewa a karkashin yarjejeniyaar da May ta cimma da EU a can baya, ko kuma a sake gudanar da wani zaben raba gardama, ko kuma dai ta fice kai tsaye ba tare da wata matsaya ba.

Yanzu haka dai Uwargida May za ta rubuta wasika ga shugaban Hukumar Gudanarwar Tarayya Turai , Donald Tusk domin neman alfarmar jinkirta ficewar kasar a dai dai lokacin da ya rage kwanaki tara kacal wa’adin ficewar ya cika a hukumance.

Sai dai kawo yanzu babu cikakken bayani game da tsawon kwanakin da May ke son Tarayyar Turai ta karawa Birtaniya kafin ficewar.

Amma fadar gwamnatin May ta ce, Firaministar ba za ta bukaci jinkiri mai tsawo ba.

Sau biyu Majalisar Dokokin Birtaniya na watsi da yarjejeniyar da May ta cimma da EU a cikin watan Nuwamba, kodayake Firaministar na fatan sake gabatar da yarjejejniyar ga Majalisar domin sake kada kuri’a a kanta a makon gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.