Isa ga babban shafi
Faransa

"Ba za mu bari Macron ya yaudare mu ba"

Faransawan da ke zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba Emmanuel Macron a birnin Paris, sun lashi takobin ci gaba da borensu tare da fadin cewa, ba za su bari shugaban ya yaudare su da shirinsa na muhawarar kasa ba.

Masu zanga-zangar sanye da riguna launin dorawa na dauki-ba-dadi da jami'an 'yan sanda
Masu zanga-zangar sanye da riguna launin dorawa na dauki-ba-dadi da jami'an 'yan sanda Zakaria ABDELKAFI/AFP
Talla

Masu zanga-zangar sun yi watsi da muhawarar watanni biyu da gwamnatin kasar ta shirya domin jin ra'ayoyin jama’a kan matakan da gwamnatin shugaba Macron e dauka.

Masu zanga-zangar sun ce, muhawarar wata dabara ce ta karkata hankulansu daga zanga-zangar da ke gudana sassan kasar.

Muhawarar ta kasa ta bai wa wadanda ke ganin cewa gwamnati ba ta kyautata musu damar bayyana ra’ayoyinsu, sannan kuma ta bai wa shugaba Macron kafar yunkurawa gabanin zabukan Majalisar Tarayyar Turai a watan Mayu.

Sai dai duk da jajircewar masu zanga-zangar, yawansu ya ragu ainun a fadin kasar, in da a yanzu mutane ‘yan kalilan ne ke halartar shataletalen da aka fara kaddamar da wannan zanga-zangar.

Sai dai duk da haka, wadanda suka jajirce wajen  ci gaba da boren, sun ce ba za su karaya ba, duba da yadda mutane da dama ke shan wahala a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.