Isa ga babban shafi
Faransa-Macron

Macron na duba yiwuwar gudanar da zaben raba gardama a Faransa

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron na duba yiwuwar gudanar da zaben raba-gardama domin kawo karshen zanga-zangar masu shudin riguna da ke adawa da matakinsa na kara farashin man fetir da dangoginsa.

Har ila yau, zaben zai nemi jin ra’ayoyin jama’a game da rage yawan ‘yan Majalisar Dokokin Kasar ko kuma a rage musu karfi
Har ila yau, zaben zai nemi jin ra’ayoyin jama’a game da rage yawan ‘yan Majalisar Dokokin Kasar ko kuma a rage musu karfi Michel Euler/Pool via REUTERS
Talla

Kafofin yada labaran Faransa sun rawaito cewa, tuni gwamnatin kasar ta buga takardun kada kuri’ar raba gardamar kan wannan batu, yayin da hukumomin kasar ke dakon umarnin shugaba Emmanuel Macron domin kaddamar da shirin zaben na ranar 26 ga watan Mayu mai zuwa, yayin da zaben zai ci karo da na Majalisar Dokokin Tarayyar Turai.

Zaben raba gardamar zai kasance irinsa na farko a tarihin Jamhuriya ta biyar a Faransa kuma takardun zaben za su kunshi tambayoyin da suka shafi tattalin arziki da al’amuran rayuwar yau da kullum.

Har ila yau, zaben zai nemi jin ra’ayoyin jama’a game da rage yawan ‘yan Majalisar Dokokin Kasar ko kuma a rage musu karfi.

Faransawa sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda shugaba Macron ya tinkari zanga-zangar masu adawa da karin haraji, abin da ya dada dakushe farin jininsa a kasar zuwa maki 27.7 daga maki 47 a cikin watanni 12 da suka shude.

Ko da yake shugaban ya yi kokarin maido da goyon bayan da yake samu daga al’ummar kasar bayan ya janye shirin nasa na karin harajin, yayin da ya shirya wata muhawarar kasa domin sauraren kuncin da masu zanga-zangar shudin rigunar suka samu kansu a ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.