Isa ga babban shafi
Faransa

Faransawa sun gaji da zanga-zangar adawa da Macron

Akalla mutane sama da 10,000 suka shiga zanga- zangar adawa da masu zanga zangar kyamar gwamnati da suka kwashe makwanni 11 suna mamaye titunan birnin Paris da wasu garuruwan Faransa.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar kawo karshen boren da ake yi wa gwamnatin Shugaba Emmanuel Macron na Faransa
Wasu daga cikin masu zanga-zangar kawo karshen boren da ake yi wa gwamnatin Shugaba Emmanuel Macron na Faransa REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Masu zanga-zangar da suka yi jerin gwano daga Dandalin Place de la Nation zuwa wurin tunawa da mazan-jiya cikin ruwan sama, sun yi ta bayyana manufofinsu, in da suke cewa, 'a ci gaba da dimokiradiya, babu juyin juya hali’, yayin da suke daga tutar Faransa da ta Kungiyar Kasashen Turai.

Mutanen da aka yi wa lakabi da masu jan kyalle, ana danganta su ne da wani injiniya daga Toulouse wanda ya gaji da yadda ake zanga-zangar adawa da gwamnatin wadda ke haifar da tahsin hankali daga masu tsattsauran ra’ayi.

Mutane da dama da suka shiga zanga-zangar sun ce, ba wai suna adawa da bukatun wancan bangaren da ke kyamar gwamnati ba ne na taimaka wa matalauta, sai dai sun gaji da yadda ake arangama da kuma lalata dukiya.

Wata mata mai suna Louise Soulie ta ce, ta amsa kiran shiga zanga-zangar ce saboda duk sun kosa a samu maslaha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.