Isa ga babban shafi
Faransa

Tarzoma ta barke a sassan Faransa yayin zanga-zanga

An yi arrangama tsakanin masu zanga zanga da ‘yan sanda a wasu sassan Faransa, bayan da a karshen mako, masu rigunan dorawa suka sake fita kan tituna a karo na 10, domin nuna adawa da shugaban kasar Emmanuel Macron.

Jami'an tsaron Faransa yayin da suka fuskanci masu rigunan dorawa da ke zanga-zangar adawa da shugabancin Emmanuel Macron. 19/1/2019.
Jami'an tsaron Faransa yayin da suka fuskanci masu rigunan dorawa da ke zanga-zangar adawa da shugabancin Emmanuel Macron. 19/1/2019. REUTERS/Jean-Paul Pelissier
Talla

Kididdiga ta nuna cewa akalla mutane dubu 84 ne suka fita zanga zangar ta jiya, inda a birnin Paris kadai, masu rigunan dorawar dubu 7, suka yi tattaki.

Wasu gungun masu zanga-zangar, sun yi ta jifan ‘yan sanda da duwatsu, da kuma kwalabe, tare da karajin kiran tilas shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi murabus.

Rahotanni sun ce a birnin Toulouse kuwa, inda masu zanga-zanga dubu 10 suka fita, an samu tarzoma, inda jami’an tsaro suka kama mutane 23, bayanda suka farfasa wani banki da kuma shaguna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.