Isa ga babban shafi

'Yansanda a Faransa sun tarwatsa masu zanga-zangar man fetur

'Yan Sanda a birnin Paris na kasar Faransa sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da ruwan zafi kan masu zanga zangar adawa da Karin farashin man fetur da gas, inda suka bukaci shugaba Emmanuel Macron da ya janye harajin.

Jami'an 'yansandan sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye wajen tarwatsa dandazon masu zanga-zangar a sassan kasar ta Faransa.
Jami'an 'yansandan sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye wajen tarwatsa dandazon masu zanga-zangar a sassan kasar ta Faransa. Lucas BARIOULET / AFP
Talla

Akalla 'yansanda 3,000 aka girke a Paris domin fuskantar masu zanga zangar wadanda suka datse hanyoyin mota a makon jiya sanye da rigar iri guda da zummar hana komai motsawa a birnin.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya bayyana cewar tun da sassafe dubban masu zanga zangar suka taru kusa da fadar shugaban kasa ta Champs–Elysees inda suka fara arangama da 'yansandan.

Rundunar 'yansandan Paris tace arangamar da aka samu na da nasaba da shigar masu tsatsaran ra’yi dake barazana ga jami’an tsaro.

A makon jiya akalla mutane 300,000 suka shiga zanga zangar inda suka tare hanyoyin motoci da hana gudanar da kasuwanci a birane da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.