Isa ga babban shafi

Takaddama ta barke tsakanin Italiya da Malta kan bakin-haure

Takaddama ta sake barkewa tsakanin kasashen Italiya da Malta, bayan da jirgin ruwan wata kungiya mai zaman kanta ya ceto bakin-haure 59 daga takun Mediterranean.

Wasu bakin-haure da kan hanyar isa nahiyar turai baya da suka tashi daga gabar ruwan Libya.
Wasu bakin-haure da kan hanyar isa nahiyar turai baya da suka tashi daga gabar ruwan Libya. AFP
Talla

Takkadamar ta biyo bayan kalaman Ministan cikin gidan Italiya Matteo Salvini, da ya ce kasar Malta ce yakamata ta karbi bakin-hauren da suka kunshi ‘yan Syria, Falasdinawa da kuma Guinea, kasancewar sun fi kusa da tashar ruwanta.

Sai dai cikin kakkausan harshe, a sakon da ya aiki ta shafinsa na twitter, Ministan cikin gidan kasar ta Malta, Micheal Farrugia, ya zargi takwaransa na italiya ta bada bayanan karya, inda ya ce Itlaiya ce ke da hakkin karbar bakin-hauren, la’akari da cewa an ceto su a tsibirin Lampedusa, wanda ya fi kusa da kasar.

Sama da bakin-haure dubu 650 ne suka isa kasar Italiya daga shekarar 2014 zuwa yanzu, mafi akasarinsu kuma an ceto su ne daga tekun Mediterranean, sai dai cikin shekarar 2018, yawan bakin-hauren da ke kwarar cikin kasar ya karu ainun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.