Isa ga babban shafi
Faransa

Tsohon ministan kasafin Faransa zai yi yarin shekaru biyu

Kotun daukaka kara a Faransa ta amince da hukuncin samun tsohon ministan kasafin kudin kasar Jerome Cahuzac na boye asusun ajiyarsa a kasashen waje domin kaucewa biyan haraji, sai dai ta rage daurin shekaru uku da aka masa zuwa shekaru biyu.

Tsohon ministan kasafin kudin Faransa Jerome Cahuzac lokacin da ake tisa keyarsa zuwa kotu kan zarginsa da boye wasu tarin kudade lokacin da ya ke rike da madafun iko.
Tsohon ministan kasafin kudin Faransa Jerome Cahuzac lokacin da ake tisa keyarsa zuwa kotu kan zarginsa da boye wasu tarin kudade lokacin da ya ke rike da madafun iko. Eric FEFERBERG / AFP
Talla

Hukuncin kotun daukaka karar ya kawo karshen kokarin tsohon ministan na sauya hukuncin karamar kotu da ta same shi da laifin boye tarin dukiya yayin da yake rike da mukami a gwamnatin Francois Hollande.

Alkalin kotun ya bayyana rage daurin da aka yi wa ministan daga shekaru 3 zuwa shekaru biyu da kuma wasu Karin shekaru biyu nan a jeka ka gyara halin ka.

Daurin shekaru biyu a Faransa bai bada damar zuwa gidan yari, sai dai a sanya mutum gudanar da wani aiki wa jama’a.

Har ila yau kotun ta kuma ci tarar tsohon ministan euro 300,000 da kuma haramta masa rike mukamin gwamnati na shekaru 5.

An dai tilastawa Jerome Cahuzac sauka daga mukamin sa ne a shekarar 2013 lokacin da aka gano cewar ya boye kudin sa a bankin kasar Switzerland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.