Isa ga babban shafi
Faransa

Gidauniyar tallafawa ma'aikata a Faransa ta samu fiye da Yuro miliyan 1

Wata Gidauniya da aka kafa a Faransa domin tallafawa ma’aikatan jiragen kasa da ke yajin aiki saboda rasa albashin su ta samu kudin da ya zarce euro miliyan guda yau juma’a.

Wasu taron masu zanga-zangar adawa da matakin shugaba Emmanuel Macron kenan a birnin Paris na kasar Faransa.
Wasu taron masu zanga-zangar adawa da matakin shugaba Emmanuel Macron kenan a birnin Paris na kasar Faransa. AFP
Talla

Kungiyar ma’aikatan kamfanin jiragen ta ce ya zuwa yau mutane sama da 26,000 suka bada gudummawa cikin gidauniyar.

Ranar 3 ga watan jiya ma’aikatan suka fara yakin aiki domin adawa da shirin shugaba Emmanuel Macron na kaddamar da sauye sauye wanda zai kai ga rage bashin euro biliyan 46 da ake bin kamfanin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.