Isa ga babban shafi
Faransa

Ma'aikatan jiragen kasa na gagarumin yajin aiki a Faransa

Ma'aikatan jiragen kasa a Faransa sun fara yajin aikin watanni uku don ci gaba da  matsin lamba ga shugaba Emmanuel Macron don ganin ya dakatar da aiwatar da shirinsa na sauye sauye.

Yajin aikin zai jefa sama da mutane miliyan hudu cikin mummunan hali
Yajin aikin zai jefa sama da mutane miliyan hudu cikin mummunan hali REUTERS/Pascal Rossignol/File Photo
Talla

Yajin aikin da Kungiyar Ma’aikatan Jiragen kasa ta kira ta ce, ba zai tsaya ba har sai shugaba Emmanuel Macron ya janye aniyarsa ta yi wa bangaren sufurin garambawul.

A karkashin tsarin yajin aikin, ma’aikatan za su rika dakatar da sufurin ne sau biyu daga cikin kwanaki 5 na aiki, wanda hakan zai jefa matafiya miliyan hudu da rabi cikin kunci.

Su ma ma’aikatan Kamfanin Jiragen Sama na Air France da masu kwashe shara da wasu ma’aikatan bangaren samar da makamashi za su fara nasu yajin aikin daga yau, yayin da Air France ya ce, kashi 75 na jiragensa ne kadai zai yi aiki,

Manyan jiragen kasa masu tsananin gudu guda bakawai za su dakatar da zirga-zirga a yayin wannan yajin aiki a kamfanin na SNCF na gwamnati, in da aka tanadi daya tal da zai yi aikin jigilar Fasinjoji.

Kazalika uku daga cikin hudu na jiragen kamfanin Eurostar zai yi aikin jigilar Fasinjoji daga Faransa zuwa London da Brussels, in da kuma jiragen Thalys da ke zuwa Belgium da Netherlands za su yi aikinsu kamar yadda aka saba, amma babu wani jirginsa da zai kwashi mutane zuwa Spain da Italiya da kuma Switzerland.

'Yan fansho da dalibai da ma’aikatan kamfanoni sun dade da fara zanga-zanga domin nuna rashin amincewarsu da sauye- sauyen shugaban kasar.

Ana saran kawo karshen yajin aikin a ranar 28 ga watan Juni mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.