Isa ga babban shafi
Lebanon

Hukumomin duniya sun yi alkawarin baiwa Lebanon agaji dala biliyan 11

A wajen wani zaman taron zuba jari da aka gudanar a yau juma’a a birnin paris bankunan da hukummin bayar da lamani na duniya sun tattara kimanin dalar Amruka biliyan 11 ga kasar Labanon da suka hada da rance da kuma tallafi, domin taimakawa  daidaita ginshikan tattalin arzikin kasar dake fuskantar barazana daga tashe tashen hankullan da ake fama da su a yankin gabas ta tsakkiya.

Sa'ad Hariri  Firaministan Labanon - da shugaban Faransa Emanuel Macron a wurin taron neman  zuba jari a Labanon
Sa'ad Hariri Firaministan Labanon - da shugaban Faransa Emanuel Macron a wurin taron neman zuba jari a Labanon Reuters/Philippe Wojazer
Talla

A wajen zaman taron da ya gudana a yau juma’a a birnin paris hukumomin kudi da kasashe masu zuba jari sun dau alkawalin tallafawa gina tattalin arzikin Labanon, inda nan take suka hada wa kasar kimanin dalar Amruka biliyan 11.

Babban Bakin duniya ya bayyana ware wa kasar sama da dala biliyan 5 da zai bata a shekara mai zuwa, domin kara karfafa ginshikan tattalin arzikin kasar ta Labanon da suka rankwafa, tare da kara bunkasa hanyoyin samar da da ayukan yi ga al’umma, kamar yadda babbar daraktar bakin, uwargida Kristalina Georgieva ta sanar.

Hukumomin dake kula da bada rance na duniya sun bayyana aniyarsu ta tallafawa kasar "bankin zuba jari na nahiyar turai ya bayyana warewa kasar EURO miliyan 800 asusun ci gaban tattalin arzikin kasashen larabawa na kasar Koweiti dala miliyan 700 M$, Bankin ci gaba da sake tada komadar tattalin arziki na nahiyar turai BERD biliyan 1, da miliyan 100 yace zai baiwa kasar a shekaru 6 masu zuwa. Sai kuma asusun ci gaban kasashen larabawa FADES, 500 na dalar Amruka

A bangaren kasashen turai kuma Fransa ta yi alkawalin bada Euro miliyan 550 Britaniya miliyan 130 Italir 120 a kungiyar tarayyar turai miliyan 150 na euro, a yayinda kasar Saudiya ta ce zuba zubawa kaar dala biliyan 1

A jimilce dai kasashe 37 da kungiyoyi 14 Au total, 37 Etats et 14 na duniya da kuma yankin gabas ta tsakkiya, hukumar bayar da lamani IMF, bankin duniya da kungiyar tarayyar turai duk sun halarci taron zuba jarin ga Labanon ana sauran wata guda a gudanar da zaben yan majalisar dokoki a ranar 6 ga watan mayun gobe a kasar ta Labaon

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.