An yi zanga-zangar adawa da kama Puigdemont a Berlin
Daruruwan mutane ne suka shiga wata zanga zangar a birnin Berlin na kasar Jamus domin bukatar ganin an saki shugaban 'yan awaren Spain, Carles Puigdemont wanda ake tsare da shi tun makon jiya.
Wallafawa ranar:
Mutanen da ke dauke da tarin lema saboda ruwan saman da aka tafka, sun yi tattaki daga kofar Brandenburg zuwa ma’aikatar shari’a, dauke da rubuce-rubucen da ke bayyana cewar, a saki Puigdemont tare da fursunonin siyasar Catalonia.
Wasu daga cikin su kuma suna dauke da tutar Catalonia mai dauke da launin ruwan bula da ruwan dorowa da kuma ja.
Hukumomin shari’ar Jamus na nazari kan bukatar Spain na mika mata Puigdemont domin fuskantar shari’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu