Isa ga babban shafi
Spain

'Yan Catalonia miliyan daya na zanga-zanga

Kimanin mutane miliyan daya ne suka yi fitar dango a birnin Barcelona da ke Catalonia, domin zanga zangar nuna rashin goyon baya kan ballewar yankin daga Spain.

Masu zanga-zanga a Barcelona, babban birnin yankin Catalonia yayin da suke tattakin nuna rashin goyon bayan ballewar yankin daga kasar Spain. 29 ga Oktoba, 2017.
Masu zanga-zanga a Barcelona, babban birnin yankin Catalonia yayin da suke tattakin nuna rashin goyon bayan ballewar yankin daga kasar Spain. 29 ga Oktoba, 2017. AFP
Talla

Masu zanga-zangar sun kuma nuna goyon baya kan matakin fara mulkar yankin kai tsaye da gwamnatin Spain karkashin Fira Minista Mariano Rajoy ta dauka, inda kuma suka bukaci a garkame tsohon shugaban na Catalonia a gidan yari, wato Carles Puigdemont wanda aka tsige.

Bayan shelar ballewa da majalisar Catalonia ta yi a Juma’ar da ta gabata, Fira Ministan Spain Mariano Rajoy, ya sanar da rusata, da kuma tsige shugaban yankin, inda ya bada umarnin shirya sabon zabe cikin watan Disamba mai zuwa.

A yau Lahadi, daya daga cikin ministocin kasar Belguim ya yi wa Puigdemont tayin bashi mafakar siyasa idan ya bukaci hakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.