Isa ga babban shafi
Spain

Spain za ta gudanar da zabe a yankin Catalonia

Gwamnatin Spain ta ce ta kammala cimma matsaya kan kwace ‘yancin cin gashin kan yankin Catalonia tare da gudanar da sabon zaben shugabancin yankin.Firaminista Mariano Rajoy, da yake zantawa da manema labarai bayan taron majalisar zartaswar kasar da ya gudana yau, ya ce za a gudanar da sabon zaben yankin nan da watanni 6 masu zuwa, amma kafin lokacin harkokin gudanarwa da ikon yankin zai dawo karkashinsa.

Firaminista Mariano Rajoy yayin taron majalisar zartaswa a yau Asabar da ya amince da kwace kwarya-kwaryan 'yancin cin gashin kan yankin Catalonia.
Firaminista Mariano Rajoy yayin taron majalisar zartaswa a yau Asabar da ya amince da kwace kwarya-kwaryan 'yancin cin gashin kan yankin Catalonia. REUTERS/Juan Medina
Talla

Tuni dai aka fara zanga-zanga a yankin na Catalonia dangane da matakin na Rajoy, yayinda a bangare guda kuma ake jiran martini daga Carles Puidgemont da ke fafutukar ganin yankin ya zama kasa mai cin gashin kanta.

A cewar Majalisar zartaswa dama sashen na 155 na kundin tsarin mulkin kasar ya amince gwamnatin ta iya kwace kwarya-kwaryan ikon gudanarwar da aka bai wa yankin matukar ya aikata wata katobara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.