Isa ga babban shafi
Spain

Zan cigaba da jagorantar fafutukar ballewa daga Spain – Puigdemont

Tsohon shugaban yankin Catalonia Carles Puigdemont da gwamnatin Spain ta tsige, ya sha alwashin cigaba da jagorantar fafutukar samun ‘yancin kan yankin daga kasar.

Tsohon shugaban yankin Catalonia Carles Puigdemont yayinda yake rattaba hannu kan takardar amincewa da ballewar yankin daga Spain, a zauren majalisar kasar da ke birnin Barcelona, ranar 10 ga watan Oktoba, 2017.
Tsohon shugaban yankin Catalonia Carles Puigdemont yayinda yake rattaba hannu kan takardar amincewa da ballewar yankin daga Spain, a zauren majalisar kasar da ke birnin Barcelona, ranar 10 ga watan Oktoba, 2017. ©REUTERS/Albert Gea
Talla

Cikin wani faifan bidiyo da aka watsa a wata kafar talabijin, wanda kuma ba'a bayyan inda aka nade shi ba, Puigdemont yayi tur da kwace ikon wani mizani na cin gashin kan yankin na Catalonia da gwamnatin Spain ta yi.

Matakin na Spain ya zo ne da safiyar yau Asabar, bayanda majalisar yankin ta goyi bayan bayyana ballewarsa daga kasar.

Tun a makon da ya gabata ne dai ma’aikatar harkokin cikin gidan Spain ta karbe iko da tafiyar da aikin rundunar ‘yan sandan yankin, bayan korar tsohon shugaban rundunar da ta yi.

A wani labarin kuma, rundunar ‘yan sandan yankin Catalonia, ta umarci jami’anta da su kasance ‘yan ba ruwanmu yayin gudanar da ayyyukansu, dai dai lokacin da ake zaman doya da manja tsakanin masu goyon bayan ballewar yankin daga Spain da kuma gwamnatin kasar.

Matakin yunkuri ne na kaucewa barkewar tashin hankali a yankin a dai dai lokacin da Spain ke kokarin kammala tilasta mulkar yankin kai tsaye, bayan da a safiyar yau majalisar yankin ta goyi bayan ballewarsu daga kasar.

Kasashen Amurka, Mexico, da nahiyar turai, sun goyi bayan matakin gwamnatin Spain, na tabbatauwar kasar a dunkule.

Sakamakon wata kuri’ar jin ra’ayi ya nuna cewa fiye da rabin mutanen yankin na Catalonia miliyan 5.3 da suka cancanci kada kuri’a basa goyon bayan ballewar da yankin ke nema daga Spain.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.