Kungiyar EU ta fara taro kan gaggauta tattaunawar ficewar Birtaniya
Yau Alhamis shugabannin kungiyar kasashen Turai 28 ke gudanar da taro a Brussels, inda zasu duba yadda tattauna ke gudana tsakanin wakilan kungiyar da na gwamnatin Birtaniya mai kokarin ficewa daga cikin ta.
Wallafawa ranar:
Ana kuma sa taron ya amince da shirin bada kudade domin dakile yadda baki ke kwarara zuwa Turai, musamman daga nahiyar Afrika.
Kungiyar kasashen Turai tace ya zuwa yanzu babu wani ci gaba da aka samu a tattaunawar rabuwa tsakaninta da Birtaniya duk da cewa an kwashe watanni 5 ana yi.
Shugaban kungiyar Donald Tusk wanda ya bayyana shakku dangane da cimma wata yarjejeniya a taron na yau, yace har yanzu Birtaniya ta gaza wajen gabatar da kwararan bukatun ta.
Tusk yace cikin kudirorin da har ya zuwa yanzu ba’a cimma matsaya akan su hada da makomar Yan kasashen Turai dake zama a Birtaniya da batutuwan da suka shafi Ireland ta Arewa, sai kuma kudaden rabuawa da kungiyar ke bukatar Birtaniya ta biya.
A wani cigaban kungiyar tayi alkawarin samar da kudade domin gudanar da wasu ayyuka a wasu kasashen Afirka cikinsu harda Nijar domin hana baki tsallakawa Turai da kuma samar da ci gaba a Yankin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu