Isa ga babban shafi
Birtaniya

Birtaniya ta nemi afuwar Turawa mazauna kasar

Birtaniya ta nemi gafafar wasu daruruwan ‘yan kasashen Turai da ke zaune a sassan kasar, bayan kuskuren aike musu da wasikun bukatar su harhada kayansu su bar kasar, kan masaniyar dokar data sahale musu zama a cikin kasar.

Firaministar Birtainya Theresa May.
Firaministar Birtainya Theresa May. Reuters
Talla

Ma'aikatar cikin gida a Birtaniyar ta ce ta kaddamar da bincike kan yadda aka yi wadannan wasiku sama da dari suka isa wajen 'yan kasashen Turai dake Zaune a Birtaniyar.

Mai magana da yawun ma'aikatar cikin gidan ta bayyana cewa lallai an samu kuskure wajen aikewa da wasikun, kuma suna tuntubar duk wadanda suka samu wasikar domin kwantar musu da hankali.

Jami'ar ta ce suna sane da cewa babu sauyi a dokar da ta bai wa 'yan kasashen Turai umarnin zama a birtaniyar.

Eva Johanna Holmberg, wata malama a jami'a 'yar asalin kasar Findland da ke auren dan Burtaniya ta ce ta kadu da samun wasikar.

'Yancin 'yan kasashen Turai na zama a Birtaniya na daga cikin batutuwa uku da kungiyar ta tarayyar Turai ke neman daddalewa da Birtaniyar kafin tattauna yadda dangantaka za ta ci gaba da kasancewa tsakanin kasashen nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.