Isa ga babban shafi
Birtaniya- EU

Birtaniya ta wallafa dokokin ficewarta daga Turai

Gwamnatin Birtaniya ta wallafa kudirin dokokinta da zai tabbatar da ficewarta daga kungiyar Tarayyar Turai. Kudirin zai yi watsi da dokokin EU sama da  dubu 12 a cikin kundin dokokin Birtaniya tare da soke dokar 1972 da kasar ta zama mamba a kungiyar.

Theresa May, Firaministar Birtaniya
Theresa May, Firaministar Birtaniya REUTERS/Eric Vidal
Talla

Kudirin watsi da dokokin na Tarayyar Turai shi ne na 8 da gwamnatin Birtaniya ta gabatar domin ficewa daga kungiyar da ta shafa shekaru 40 a matsayin mamba.

A watan jiya da wakilan Birtaniya da Tarayyar Turai suka soma tattauna batun ficewar kasar daga kungiyar, bangarorin biyu sun samu sabani kan makomar ‘yan kasashen tarayyar Turai a Birtaniya.

Daya daga cikin fannin da bangarorin biyu ke da sabani shi ne kan makomar Birtaniya a kotun Turai, akan ko kasar za ta ci gaba da bin sharuddan kotun?

Sabon kudirin da Birtaniya ta wallafa a yanzu, zai soke dokar 1972, lokacin da ta zama mamba a tarayyar Turai tare da yin watsi da dokokin kungiyar dubu 12 da Birtaniyar ke amfani da su.

Babban kalubalen da ake ganin ke gaban Firaminista Tharesa May shi ne, kare sabbin dokokin musamman ayar dokar da ta ba Ministoci karfin ikon sauya dokokin Turai ba tare da yawun Majalisa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.