Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta cafke masu fataucin ‘yan ci-rani

Jami’an tsaro a Faransa, sun cafke wasu ‘yan kasar Sudan da suka share tsawon lokaci suna fataucin baki ‘yan ci-rani zuwa cikin Faransa da sauran kasashen yankin Turai ta barauniyar hanya.

Fataken sun shigar da bakin haure akalla 645 a cikin kasashen Faransa da Birataniya da Jamus da kuma wasu kasashen Turai.
Fataken sun shigar da bakin haure akalla 645 a cikin kasashen Faransa da Birataniya da Jamus da kuma wasu kasashen Turai. REUTERS
Talla

Majiyar ‘yan sanda a Faransa, ta ce an cafke ‘yan Sudan 7 da wani dan kasar Tunisia daya, wadanda daga watan Janairu zuwa Oktoban bana suka shigar da bakin haure akalla 645 a cikin kasashen Faransa da Birataniya da Jamus da kuma wasu kasashen Turai.

An share tsawon watanni 9 ana gudanar da bincike kan wadannan mutane kafin cafke su, kamar dai yadda shugabar sashen kula da yaki da masu aikata manyan laifufuka a ma’aikatan ‘yan sanda Nathalie Dellali ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Mafi yawa daga cikin mutanen da wadanda ake zargin suka shigar a yankin na Turai sun biya kudade a hannun fataken, da yawansu ya kama daga yuro 500 zuwa Euro dubu biyar a cewar ‘yan sandan.

A lokacin wani samame kuwa, ‘yan sandan sun gano jikunan matafiya da aka boye a gidajen cin abinci da na sayar da barasa, kuma ga alama ana tsara yadda za a wuce da matafiyan ne zuwa wasu kasashe na Turai daga Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.