Isa ga babban shafi
Libya

‘Yan ci-rani na fuskantar azaba a Libya

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce akwai ‘yan ci-rani sama da dubu 20 da suka kunshi mata da yara kanana da aka kama ake tsare da su a garin Sabratha na Libya, inda rahoton ya ce ‘Yan ci ranin fuskantar cin zarafi da azabtarwa daga masu kokarin fataucinsu zuwa Turai.

Wani sansani da ake tattara 'yan ci-rani a Gharyan cikin kasar Libya
Wani sansani da ake tattara 'yan ci-rani a Gharyan cikin kasar Libya REUTERS/Hani Amara
Talla

An bi gida gida da gonakki ne aka tattaro ‘yan ci ranin bakaken fata ‘yan Afrika, kuma rahoton da hukumar kula da ‘yan gudun hijirar ta fitar ya ce ana tsare da su ne a Sabratha garin da ya yi kaurin suna wajen fataucin mutane zuwa Turai.

Rahoton ya ce hukumomin Libya na tsare da ‘yan ci ranin kusan budu 15 a Sabratha wadanda a can baya suka kasance fursunoni ko kuma bayin masu fatauci.

Yawancinsu Mata ne da ke dauke da jinjirai wadanda aka ajiye a wani sansani kuma da ke samun tallafi daga kungiyoyin agaji.

A daya bangaren kuma rahoton ya ce akwai wasu sama da dubu 6 da masu fatauci ke tsare da su wasu wurare da ba a bayyana ba a yankin na Sabratha.

Wadanda dai suka samu suka tsira da ke karkashin kulawar gwamnati sun shaidawa jami’an agaji irin ukubar da suka fuskanta ta cin zarafi da azaba a hannun masu fataucin.

Wasu da dama an same su ne cikin yanayi na yunwa inda suka ce sun shafe kwanaki ba abinci sannan ba tufafin da za su sirinta jikinsu saboda tsananin wahala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.