Isa ga babban shafi
Austria

Ana gab da samun shugaba mafi karancin shekaru a duniya

Rahotanni daga Austria na nuni da cewa matashin dan takarar shugabancin kasar Mr Sebastian Kurz na kan gaba da yawan kuri’u a babban zaben ke gudana yau Lahadi.Dankarar Jam’iyyar masu ra’ayin rikau Mr Sabestian Kurz na kan gaba da kuri’u kashi 31.5 yayinda jam’iyyar masu zazzafan ra’ayi ke biye masa baya da kuri’u kashi 27.1 sai kuma jam’iyyar ‘yan burguzu mai kashi 25.9.

Dankarar Jam’iyyar masu ra’ayin rikau Mr Sabestian Kurz mai shekaru 31 na kan gaba da kuri’u kashi 31.5.
Dankarar Jam’iyyar masu ra’ayin rikau Mr Sabestian Kurz mai shekaru 31 na kan gaba da kuri’u kashi 31.5. REUTERS/Leonhard Foeger
Talla

Matukar dai Mr Kurz mai shekaru 31 ya yi nazara a zaben na yau zai zamo shugaba mafi karancin shekaru a Nahiyar Turai dama duniya baki daya.

Kafin tsayawarsa takarar shugaban kasa, Mr Kurz ya rike ministan harkokin wajen kasar a shekarar 2013 yana da shekaru 27.

Daga bisani ne kuma Mr Kurz mai tarin magoya baya a ciki da wajen kasar ya zama madugun jam’iyyarsa cikin watan watan Mayun shekarar nan.

Ana dai yiwa Mr Kurz lakabi da ‘‘Wunderwuzzu’’ ma’ana wanda zai iya tafiya akan ruwa, yayinda ake kwatanta kwarjininsa da na matasan shugabannin Duniya na yanzu wato Emmanuel Macron na Faransa da Justin Trudeau na Canada.

Haka zalika Mr Kurz ya kasance mai ra’ayin salon shugaba Emmanuel Macron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.