Isa ga babban shafi
Iran

Ana zaben shugaban kasa a Iran

Al’ummar Iran na gudanar da zaben shugaban kasa a yau Juma’a inda ake fafatawa tsakanin shugaba Hassan Rouhani da ake yi wa kallon mai sassaucin ra’ayi da Ebrahim Raisi mai tsattsauran ra’ayi.

Ali Khamanei ya kada kuri'arsa a zaben shugaban kasa
Ali Khamanei ya kada kuri'arsa a zaben shugaban kasa DR
Talla

Tun karfe 8 na safe aka bude runfunan zabe, kuma ana bude runfunar zaben shugaban addinin kasar Ayatollah Ali Khameni ya kada kuri’arsa.

Shugaba Rauhani na fuskantar kalubale daga Raisi mai tsattsauran ra’ayi akan alakar Iran da kasashen yammaci.

Kasashen duniya sun zuba ido domin ganin yadda zaben zai kaya, musamman saboda rawar da Iran ke takawa a siyasar duniya.

Zaben kasar Iran na da matukar tasiri ga kasashen duniya, musamman ganin rawar da shugaba Hassan Rouhani ya taka wajen kulla yarjejeniyar nukiliya da kasashen duniya domin cirewa kasarsa takunkumi.

‘Yan kasar Iran da kasashen duniya na kallon Rouhani a matsayin mai saukin ra’ayin da za a iya tafiya da shi a harkokin duniya.

Sai dai kuma batutuwan cikin gida da suka hada da rashin ayyukan yin matasa da kuma matsalar tattalin arziki sakamakon faduwar farashin mai da kuma zuba jari da ba su inganta ba na yin barazana ga sake zabensa.

Raisi wanda ya amince da ci gaba da yarjejeniyar da Iran ta kulla na nukiliya, ya ce Iran ta bada kai sosai ga kasashen Yammacin duniya.

Masu sharhi na kallon Raisi a matsayin wanda alakarsa da kasashen Yammacin duniya ba za ta dore ba, musamman ganin nasarar da Rouhani ya yi a mulkin sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.