Isa ga babban shafi
Iran

Rouhani ya yi rajistar tsayawa takara a Iran

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya yi rajistar neman sake tsayawa takara a zaben shugabancin kasar da za a gudanar a watan gobe.

Shugaban Iran  Hassan Rohani na neman sabon wa'adi kan karagar mulki
Shugaban Iran Hassan Rohani na neman sabon wa'adi kan karagar mulki © Reuters
Talla

Yanzu haka dai shugaba Rouhani zai fafata da Ebrahim Raisi da ke da kusanci da jagoran addinin kasar Ayatollah Khamenei.

Kazalika tsohon shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad na cikin ‘yan takara a zaben wanda za a gudanar a ranar 19 ga watan Mayu mai zuwa.

A shekarra 2013 ne Rouhani ya lashe zaben kasar da gagarumin rinjaye, yayin da gwamnatinsa ta cimma yarjejeniyar makamin Nukiluya da manyan kasaahsn duniya 6, in da Iran ta amince ta dakatar da shirinta na mallakar Nukiliya don janye takunkuman tattalin arziki da aka kakaba ma ta.

A jiya Juma’a ne dai shugaban ya yi rajistar neman sabon wa’adi kan karagar mulki, yayin da ake zaton Ebrahim Raisi zai iya shan gabansa a zaben na watan gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.