Isa ga babban shafi
Turai

FIFA ta yi watsi da bukatar rijistar Adrien Silva zuwa Leicester

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta yi watsi da rokon da hukumar kwallon kafar Ingila ta shigar gabanta na neman dawo da Adrien Silva daga Sporting Lispon zuwa Leicester City. Leicester ta mika takardun yarjejeniyar sayen Silva kan kudi fam miliyan 22 ne bayan dakika 14 da rufe kasuwar musayar 'yan wasa ranar 31 ga watan Augusta, lamarin da ya sa FIFA ta ki bayar da takardar shaidar cinikin.

Bayan dakika 14 ne kulle kasuwar cinikayyar 'yan wasa Leicester City ta mika bukatar sayen Andrien Silva daga Sporting Lispon.
Bayan dakika 14 ne kulle kasuwar cinikayyar 'yan wasa Leicester City ta mika bukatar sayen Andrien Silva daga Sporting Lispon. Reuters
Talla

A cewar hukumar ta FIFA matukar Leicester na bukatar Andrien dole ta jira zuwa lokacin da za a bude kasuwar cinikayyar ‘yan wasa amma babu yadda za a yi ta iya yi mishi Rijista a halin yanzu .

Duk da cewa Adrien mai shekaru 28 dan kasar Portugal ya halarci kallon wasan da kungiyar ta fafata Porto a lahadin da ta gabata, amma ba a bashi damar taka leda ba haka zalika ba a bashi damar gudanar da atisaye tare da ‘yan wasan kungiyar ba.

Yanzu haka dai sai an bude kasuwar cinikayyar 'yan wasa cikin watan Janairu ne Leicester za ta iya saka Silva a jerin 'yan wasanta bayan FIFA ta bayar da takaddar shaida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.