Isa ga babban shafi
Jamus

Markel ta lashe babban zaben Jamus

Jam’iyyar Angela Merkel ta yi nasara a zaben ‘yan majalisar dokokin Jamus da aka gudanar a jiya Lahadi, abin da ya bata damar ci gaba da rike mukaminta na shugabar gwamnatin kasar karo na hudu a jere.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da mukarrabanta.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da mukarrabanta. @Reuters
Talla

Jam’iyyar masu ra’ayin rikau ta AFD kuwa, karon farko ta yi nasarar shiga zauren majalisar dokokin kasar.

Kawancen jam’iyyun CDU da CSU da ke mara wa Angela Merkel baya a wannan zabe, ya lashe sama da kashi 33 cikin dari na kuri’un da aka jefa a zaben na jiya, abin da ke ba ta damar ci gaba rike wannan matsayi da ta share tsawon shekaru 12 tana kansa.

Babbar jam’iyyar hamayya ta Social Democrats da Martin Schulz ke jagoranta, ta samu kuri’un da yawansu ya kama daga kashi 20 zuwa 21 cikin dari, kamar dai yadda wannan sakamako da ba na dindindin ba ya nuna.

Ita kuwa jam’iyyar nan ta masu nuna kiyayya ga addinin musulunci da kuma bakin-haure AFD, ta lashe kashi 13 cikin dari, wanda shi ne karo na farko a tarihi da ta taba samu wannan kaso da ke ba ta damar samun kujeru a cikin zauren majalisar dokokin kasar ta Jamus.

Tuni dai jam’iyyar Social Democrats, ta sanar da cewa ba za ta kulla kawance domin shiga gwamnatin da Merkel za ta kafa ba, inda a maimakon haka, ta zabi shiga a cikin gungun ‘yan adawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.