Isa ga babban shafi
Jamus

Al'ummar Jamus na kada kuri'a a babban zaben kasar

Yau Lahadi al’ummar kasar Jamus ke kada kuri’unsu a zaben shugabancin kasar, da masu hasashe ke kallon mai yiwuwa shugabar gwamnatin kasar Angela Markel, ta sake zarcewa karo na hudu.

Al'ummar kasar Jamus sun fara kada kuri'a a babban zaben kasar.  (Daya daga cikin rumfunan zabe a birnin Berlin) 24 ga Satumba, 2017.
Al'ummar kasar Jamus sun fara kada kuri'a a babban zaben kasar. (Daya daga cikin rumfunan zabe a birnin Berlin) 24 ga Satumba, 2017. REUTERS/Fabrizio Bensch
Talla

Sai dai sakamakon wata kuri’a jin ra’ayin jama’a ya nuna cewa, ba lallai bane jami’iyyar Markel ta CDU, ta samu rinjaye a majalisar kasar kamar baya.

Hakan kuwa na da nasaba da cewa har zuwa yau da aka fara zaben, kuri’ar jin ra’ayin ta nuna cewa akalla kashi daya bisa uku na Jamusawan, basu tantance wanda zasu jefawa kuri’arsu ba, tsakanin jam’iyyar CDU ta Markel da ta abokin hamayyarta na SPD wato Martin Schulz.

Zalika ana sa ran ganin jami’yyar adawa ta AFD, ta samu nasarar lashe kujeru da dama zauren majalisar kasar, bayan nasarar samun kaso mai yawa a zaben kananan hukumomin kasar da ya gudana a shekarar da ta gabata.

A waccan lokacin, msharhanta sun danganta nasarar da AFD ta yi da yadda farin jinin Angela Markel yayi kasa a tsaknin wasu 'yan kasar, sakamakon matakin da gwamnatinta ta dauka na budewa Bakin-haure kofar shiga kasar, duk kuwa da rashin aminta da hakan da suka yi cikin harda jam'iyyun adawa.

Dubban bakin haure ke kwarara zuwa Turai ta tekun Bahrum
Dubban bakin haure ke kwarara zuwa Turai ta tekun Bahrum Angelos Tzortzinis / AFP

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.