Isa ga babban shafi
Faransa-Jamus

Jamus da Faransa sun bukaci daukar matakin bai-daya kan ‘Yan ci-rani

Daruruwan baki ‘Yan ci-rani sun fara shiga kasashen Turai ta hanyar Serbia a yayin da Shugabannin Faransa da Jamus suka bukaci daukar mataki na bai-daya tsakanin kasashen Turai domin magance matsalar kwararar ‘yan ci-ranin.

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da François Hollande na Faransa, à Berlin.
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da François Hollande na Faransa, à Berlin. REUTERS/Axel Schmidt
Talla

‘Yan gudun hijira sama da 2000 ne suka fara bi ta kasar Serbia zuwa kasashen Turai bayan dubbai da ke bi ta Macédonia.

Shugaban Faransa Francois Hollande ya ce dole ne su amince da matakin bai-daya domin magance matsalar kwararar bakin hauren, da Tarayyar Turai ta bayyana adadi mafi girma tun yakin duniya na biyu.

Hollande ya ce suna bukatar tsawon lakaci domin shawo kan matsalar bakin hauren da ke ci gaba da kwarara zuwa Turai.

Kasar Jamus ta yi shirirn karban bakin haure kimanin dubu 800 a bana, amma yanzu haka al’ummar kasar sun fara zanga-zangar kyamar ‘yan ci-ranin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.